Monday, June 26, 2017
NAZARIN LITTAFIN JIKI MAGAYI A BISA MAZHABAR XANGAMBO
Share fage
A nan za a yi nazarin littafin zube ne mai suna Jiki Magayi. Za kuwa a yi nazarin ne ta hanyar bin matakan nan na nazarin qagaggen labari na zube wanda Shehin malami Xangambo ya tsara. Shehin malamin ya kawo matakai guda bakwai da yake ganin su ya kamata abi wajen fexe littafin zube. Don haka waxannan matakai su ne za a bi xaya bayan xaya, wajen wannan nazari. Na san an sha yin nazarin wannan littafi sai dai kusan duk nazarin da ake yi an fi mayar da hankali ga fitar da jigo kawai da kuma zubi da tsari na labarin. Wanda a hakan ma ba akan bi su filla–filla daki – daki ba. Don haka, a ganina ya kamata a faxaxa nazarin wannan littafi domin fito da sauran hikimomin da waxannan marubuta suka qunsa a cikin littafin. Ga matakan da za a xora nazarin ko wannan fixa a kan su:
Share fage (gabatarwa)
Tarihin mawallafi
Sharhi a kan jigon littafi
Sharhi a kan zubi da tsarin littafi:
Zubi da tsari na gaba xaya
Zubi da tsarin filla – filla
Tsarin jumloli
Tsarin sakin layi
Tsarin babi – babi
Tsarin qulla labari
Sharhi a kan salon littafi:
Salon littafi na gaba xaya
Salon filla – filla:
Dabarun jawo hankali:
Ba xoki
Xaga hankali
Amfani da addini
Hoton zuci (hoto cikin bayani)
Lokacin da labari ya auku
Amfani da hotuna da zane – zane
Jerin daidaiton lafazi daga jerin bambantonsa
Dabarun sarrafa harshe:
Amfani da azancin zance
Amfani da kalmomi cikin hikima
Kalmomin aro
Tsofaffin kalmomi (tsohuwar Hausa)
Karin harshe
Ginin jumloli
Sharhi a kan mutanen cikin labari:
Sunayensu da siffofinsu
Yanayinsu, matsayinsu da halayensu
Sharhi a kan babban tauraron labari
Kimar jimilla: (sharhi a kan ingancin littafin) (Gusau, 1995:54).
Tarihin Mawallafi
Wannan littafi ne da mutum biyu suka haxa gwiwa wajen rubuta shi. Wato R. M East da kuma John Tafida Wusasa. R. M. East, cikakken sunansa shi ne Rupert Moultrie East. An haife shi a birnin London da ke qasar Ingila a shekarar 1898. Mahaifinsa shugaban (pasto) wata coci ce da ke Shrivhnon a gundumar Oxford ta qasar Ingila. Mahaifiyarsa, sista ce a wannan cocin. Mahaifan East dukkaninsu mabiya xariqar Katolika ne. Mr East ya zo Nijeriya a shekarar 1923 a matsayin xan mulkin Mallaka daga qasar Ingila. Ya zauna a Arewacin Nijeriya a garuruwan Adamawa, da Benuwai, da kuma Zariya a qarqashin ma’aikatar Ilimi. Ya yi aikin koyarwa da kuma shugabantar Hukumar Talifi da Kamfanin Gaskiya na tsawon shekara Ashirin da Takwas (28). Wanda a shekarar 1958 ya yi ritaya daga aikin mulkin mallaka, ya koma qasar Ingila. Ya mutu ranar 3 ga watan Yuni, 1975. Ya bar matan aure biyu da ‘ya’ya biyu. (Ahmad, 2010:181).
Shi kuwa John Tafida Wusasa an haife shi ne a cikin birnin Zariya a shekarar 1915. Cikakken sunansa shi ne John Tafida, kuma jikan Sarkin Zazzau ne. Ya fara karatunsa na farko a Wusasa ta Zaria C.MS 1922. Bayan gama karatunsa dai ya kama aiki da Kamfanin Gaskiya Corporation, Zaria, a matsayin Edita har 1955. Lokacin da yake aiki a can ne ya rubuta wannan littafin na Jiki Magayi. An rubuta littafin ne a sakamakon shiga gasar rubuta qagaggun labarai na Hausa da aka shirya a shekarar 1933.
Bayan nan ya tafi qasar Moscow, domin koyar da harshen Hausa a Jami’ar Moscow. Ya kuma yi aiki a Sashen Hausa na Rediyon Moscow a 1961. Malam John Tafida ya rasu a Wusasa a shekara ta 1984.
Jigon Littafin Jiki Magayi
Labarin Jiki Magayi na da jigo ne tahaqiqi wanda akan iya gano shi ta bin waxannan matakai, watau la’akari dangane da manufa da kuma dangane da mutane. Game da manufa ana duba wacce manufa ce ta fi, akan kuma duba ta dangane da tushen manufar da kuma mamayewa. Ana iya gane manufar da ta fi in an kwatanta da sauran manufofi na labarin. Bari mu duba manufar wannan labari don ganin wacce ta fi. Ya tushenta yake kuma ya mamayewarta take a labarin.
Manyan manufofin labarin Jiki Magayi:
Dangantakar Abubukar da Zainabu, watau Soyayya.
Tsananin son haihuwa da malam Shehu ya yi a littafin.
Mafarkin Malam Shehu ya taka muhimmiyar rawa a labarin.
Malam Shehu ya yi wa Zainab magani don ya aure ta.
Tasirin magani a kan
Subscribe to:
Posts (Atom)
GASKIYA INA LAIFINKI? Daga Aliyu Muhammadu Bunza
1. Shukuran ga Allah wahidun mai agaji, Da salati gun Manzo aminin shiriya. 2. Na yo yabo matuqa dukan asahabihi, Manyan gwaraje m...
-
Wasan kwaikwayo wani ~angare ne a cikin adabin Hausa, wanda ya ta~o dukkanin harkokin rayuwar ]an Adam ta yau da kullum domin yana bayya...
-
Share fage A nan za a yi nazarin littafin zube ne mai suna Jiki Magayi. Za kuwa a yi nazarin ne ta hanyar bin matakan nan na nazarin qagag...
-
Daga Mustapha Hamid ‘Yar shugaban wata ƙungiyar asiri, mai aƙidar auratayya birjik, mai suna Warren Jeffs ta ce, Mahaifin nata yayi ta ...