Aurar da yara mata da zarar sun balaga ko kuma kafin ma su balaga, yana daga cikin halayen magabata na kwarai. Kuma yana daga cikin hanyoyin da zamu iya bi a wannan zamanin domin dakile barna da ayyukan fasikanci wadanda kullum suke kara yaduwa a cikin al’umma. Ba kamar yadda Turawan yamma kullum suke kokarin juyar da tunanin al’ummar Musulmai ba, suna cewa wai aurar da ‘ya’ya mata da wuri yana haifar da cututtuka, yana haifar da lalacewar rayuwa da sauran matsaloli kala-kala, wanda kuma duk karya ce zalla. Kuma hujjojin da suke bayarwa a kan haka ba karbabbu bane, tunda cututtukan da rashin auren ke haifarwa sun fi girma sannan sun fi muni fiye da duk tunanin mutum.
Yarda da irin wadannan miyagun ra’ayoyin na Turawa ya kan sanya wasu daga Jama’ar Musulmai, wadanda suke ganin wai kansu yawa ye, har suna kallon addininmu da kyawawan al’adunmu kamar wani ci baya. Su kansu turawan idan kun duba cikin tarihinsu da tarihin sarakunansu da daulolinsu za ku tarar cewa cike suke da tarihin ‘ya’yan sarakunansu wadanda aka aurar da wuri, har ma sukan hayayyafa kuma su turawan suna alfahari da su.

Su turawa a ra’ayinsu zina ba laifi bane mutukar dai an yi ta ne bisa soyayya, ko kuma kan ra’ayin masu yin ta, idan ba tilastasu aka yi ba. Shi ya sa su a wajen su aure bashi da wani muhimmancin da za a kula da shi wajen tsaftace al’umma. Amma shi aure shi ne jigon rayuwa tunda ta dalilinsa ne ake samun yaduwar al’umma managarciya. Kuma aure ibada ne tunda ta hanyarsa a kana samu shiga Aljanna.
Aure yana tsaftace al’umma ya hana barna shiga cikinta. Kuma aure yana gyara halayen masu yin sa, ya hana su afkawa cikin sabon Allah. Abu ne mai hatsari a rika jinkirta ma ‘ya’ya mata yin aure don burin neman abin duniya. Ko dai a ce wai sai ta gama makaranta ta samu aiki, ko kuma a ce ba za a aurar da ita ga talaka. Ana jiran mai kudi ya zo ya aureta. Ba a la’akari da hali ko yanayin da ita yarinyar za ta iya shiga saboda sha’awa ko matsuwarta da yin aure.
Wannan duk tsari ne irin na Yahudu da Nasara wadanda mafiya yawansu sukan kare kuruciyarsu ne ba tare da yin aure ba. Kuma ba su kawo tunanin mutuwa a zukatansu ballantana su yi tanadi dominta.
Ya zama wajibi iyaye kuji tsoron Allah ku rika bin dokokinsa wajen aurar da ‘ya’yanku da zarar sun samu manemi na kirki koda kuwa ba su kammala karatun bokon ba. Idan shi mijin ya so sai su koma su ci gaba da karatunsu tare da aurensu. Wannan shi ne ya fi alkairi da kuma kiyaye tarbiyyarsu daga lalacewa.
Read More at: https://hausa.leadership.ng/2018/10/05/faidar-yin-aure-da-wuri/
Read More at: https://hausa.leadership.ng/2018/10/05/faidar-yin-aure-da-wuri/
No comments:
Post a Comment