Rediyo kamar yadda sunansa ya ke a Turanci,
wata hanya ce ta isar da sa}o ga jama’a na kusa da kuma na nesa, ta hanyar jin
sauti ba tare da ganin mai isar da sa}on ba. Rediyo yana ]aya daga cikin
hanyoyin mafi sau}i da kuma sauri da ]an Adam ya tanadar wa kansa don biyan
bu}atar isar da sa}onni da ilimantarwa da fa]akarwa da kuma nisha]antarwa. Wa]annan
abubuwa guda uku su ne babban ma}asudin kafa gidan rediyo ga jama’a a duniya.
Gidan rediyo yana ]aya daga cikin kafafen watsa labarai da ]an Adam ya }ir}iro
don taimakawa kansa wajen sadarwa.
Shekaru da dama da suka wuce ]an Adam yana da
hanyoyin sadarwa daban-daban na gargajiya kamar ihu da kuka da yekuwa da buga
wani abu ko ki]a ko kuma busa }aho.
An samu ci gaba a inda ]an Adam ya iya rubutu
da karatu daga nan sai ya fara amfani da rubutun yana aikawa da sa}o ta hanyar
wasi}a a rubuce, ta haka har aka samu wasi}a mai suna kar-ta-kwana.
Ana kyautata zaton cewa wani Bature mai suna Macconi
wanda yake injiniya ne, shi ne ya fara }ir}iro wayar iska tare da yin gwajinta
a cikin shekarar 1899, a New York ta }asar Amurka. Wannan }ir}ira ita ta haifar
da rediyo ko kuma ilmin }ir}irar rediyo da ake amfani da shi a yau.
A don haka wannan ci gaba na zamani da ]an
Adam ya samu ta rayuwa, shi ya bayyana samar da rediyo a ko’ina, a ciki har da
Nijeriya. Gidan rediyo na farko da aka fara bu]ewa a Nijeriya shi ne Nigerian
Broadcasting Services (NBS) a shekarar 1962, a garin Legas. Wannan gidan Rediyo
(NBS) daga baya an canza masa suna zuwa Nigerian Broadcasting Cooperation
(NBC), daidai wannan lokacin Nijeriya tana da yankuna guda uku, don haka sai
aka yi tashoshi na rediyo a wa]annan ~angarori guda uku, jihar Gabas, da Yamma
da Arewa. Wannan shi ne ya haifar da a ranar sha biyar ga watan Maris 1962, aka
bu]e Gidan Rediyon Tarayya na Kaduna.
Alh. Sir, Ahmadu Bello Sardaunan Sakkwato, kuma Firimiyan Jihar Arewa, ya
bayyana muhimman abubuwa guda uku ake bu}ata a gidan rediyon ya yi wa mutane
Arewa. Ga abin da Firimiya ya ce a wajen bu]e wannan gidan Rediyo. Wannan gidan
rediyon kamar sauran gidajen rediyo, ana sa ran ya ilmantar, ya nisha]antar ya
kuma sanar game da nisha]antarwa kuma akan ce, ta~a ki]a ta~a karatu”.

Har ila yau, a shekarar 1976 gwamnatin soja ta
Tarayya ta rushe kamfanin NBC ta sake kafa Federal Redio Corporation of Nigeria
(FRCN) aka kuma raba yankin Ibadan da Ikko da kuma yankin Kaduna.
Gidan Rediyon Nijeriya na Kaduna shi ne kusan
jagoran sauran gidajen rediyo domin kuwa duk sauran gidajen rediyon Nijeriya ta
Arewa musamman }asashen Hausa a }ar}ashin yankin Rediyo Kaduna suke. An tabbatar
da cewa ta hanyar amfani da rediyo ne za a iya sanar da al’umma abin da
gwamnati take ciki tare da ilmantarwa da nisha]antarwa. To ta yin la’akari da
haka ya sa wasan kwaikwayo ya zama wata muhimmiyar hanya mafi sau}i wajen isar
da sa}o ga al’umma.
Wannan dalili ya sa ake ganin cewa an da]e ana
yin wasan kwaikwayo a gidajen rediyon }asar nan. Ana iya cewa wasan kwaikwayo
na rediyo an fara shi tun wajen shekarar 1954, amma a nan arewancin Nijeriya
ana ganin cewa wasannin kwaikwayo na farko da aka fara gabatarwa a rediyo, an
fara su ne a rediyon Tarayya na Kaduna a cikin shekarar 1963. Shirin Noma yanke
Talauci, shi ne shiri na farko da aka soma gwadawa cikin shirin wasan
kwaikwayo. Dalilin kiran shi wasan kwaikwayo shi ne saboda ana gabatar da shi
ne ta yin amfani da yanayin wasa da raha da masu gabatarwar suka yi domin jan
hankalin manoma don koyar da su dabarun noma irin na zamani.
Daga wannan shiri kuma sai wasan kwaikwayon
“Zaman Duniya Iyawa Ne”. Shi wannan shiri, wani madubi ne na rayuwa, kuma don
kada a bar masu saurare da wasan kwaikwayo guda ]aya wanda ya shafi aikin gona
kawai sai wani shirin ya fito wanda Alhaji Yusuf Ladan ya rubuta na tsawon
shekaru. Wannan shirin yana }unshe da ban dariya da nisha]antarwa.
Daga nan kuma sai aka samu wasan kwaikwayo
“Taba sa Farin Cikin Aljihu. Kamfanin Taba Sigari sun sadu da Hukumar Gidan
Rediyon Tarayya Kaduna suka bu}aci marubucin wasan Zaman Duniya Iyawa ne ya
rubuta wannan wasa na ‘Taba sa Farin Cikin Aljihu’. Wannan shirin ya yi matu}ar
kar~uwa don kuwa an sami manoma da dama da suka rungumi noman Taba a wancan
lokacin.
Da tafiya-ta-yi-tafiya kuma sai aka fito da
wani shiri mai suna “Basafce [an Mallam Dogara na Kumatu Mai Karen Kamun Kura”.
Shi wannan wasa ne da ya ke koyar da aikin gona da kiwon lafiya don zama cikin
}oshin lafiya. Bayan wannan kuma sai shirin “Gundumi Fasa Kwanya” wasa ne wanda
Alhaji Yusuf Ladan ya shirya. Wasan ya shafi dambe na gargajiya. Haka kuma wasa
ne wanda ya zama tamkar zakaran gwajin dafi. Wannan wasa ya yi matu}ar amsuwa
ga al’ummar Arewacin Nijeriya kuma ya }ara fito da wannan Gidan Rediyo Tarayya
na Kaduna.
Daga nan kuma a cikin shekarar 1972 sai wasu
shirye-shirye su ka samu wa]anda suka }ara wa harkar wasan kwaikwayo ha~aka a
wannan gidan rediyo Nigeria na Kaduna. Wa]annan shirye-shiryen sun ha]a da;
shirin Duniya Budurwar Wawa, da Samanja Mazan Fama, wa]anda Usman Baba Pategi
yake shiryawa.
Hakan ya taimaka wajen samuwar wasannin
kwaikwayo a gidajen Rediyo na jihohin Arewacin }asar nan, misali idan muka dubi
gidan Rediyon Kano wato gidan Rediyon da yake bi wa na Kaduna wajen iya gabatar
da shirye-shirye, sun yi }o}ari fiye da yadda ake tsammani ta fuskar shirya
wasannin kwaikwayo. Wasu daga cikin ire-iren wasannin kwaikwayo da aka gudanar
a wannan lokacin sun ha]a da. In Ba Ku Ba Gida; wanda Mrs. Afinike Hamman wata
mutuniyar Bauchi ta ke shiryawa tare da taimakon Hassana Umaru da Kulu
Suleiman, kuma akwai wasanni kamarsu; Komai da Ruwanka” wanda Mallam Sharif
Lawal Adamu ya shirya, sai kuma wasan “Duniyar Nan Tamu” na Malam Abdullahi
Sani Makarantar Lungu, Haka kuma akwai wasan “Hannu [aya” wanda shi gidan
Rediyo ya ke shiryawa, akwai kuma wasan “Jami’ar Fanisau” wanda yana }unshe ne
da raha kuma sukan shirya shi ne domin yin shagu~e ga Gwamnati. Sauran wasanni
da aka gabatar a wannan gidan rediyo sun ha]a da; Jatau Na Albarkawa; da Jatau
na {yallu, da sauransu.
Haka kuma Gidan Rediyon Jihar Bauchi ya
gudanar da wasu wasannin kwaikwayo da suka ha]a da; “Duniya Ina Za Ki Da Mu”
wanda Abubakar Aliyu Dori yake shiryawa, da kuma wasan “Yaro Sabon Mutum, wanda
Hauwa Muhammad Bin take shiryawa.
Da haka dai wasannin
kwaikwayo su ka yi ta ci gaba da ya]uwa da ha~aka a gidajen Rediyo daban-daban
na jiholin Arewacin Nijeriya, kuma kodayaushe ana samun sababbi idan bu}atar
yin hakan ta samu. Ko a halin yanzu ana gudanar da wasannin kwaikwayo a
gidajen Rediyo da dama wa]anda suke a
jihohin Arewacin }asar nan ciki har da Gidan Rediyon Jihar Kebbi wanda ake
gudanar da wannan bincike a kan sa. Wasannin sun kasance wata hanya ko wata
kafa ta nisha]antarwa da fa]akarwa tare da ilmantarwa ga dukkanin al’ummomin da
ke zaune a wa]annan jihohin.
[1]
Tattaunawar da aka yi
da wasu ma’aikatan Gidan Rediyon Jihar Kebbi ranar 10/11/2018 a gidan Rediyo.
No comments:
Post a Comment