Wasan kwaikwayo wani ~angare ne a cikin adabin Hausa,
wanda ya ta~o dukkanin harkokin rayuwar ]an Adam ta yau da kullum domin yana
bayyana wa mai kallo ko sauraro ko karatu hanyoyin rayuwar jama’a ta fuskar
sana’oinsu da yanayin zamantakewarsu da al’adunsu.
Ma’anar Wasan Kwaikwayo
Masana da manazarta da dama sun tofa
albarkacin bakinsu dangane da ma’anar wasan kwaikwayo kamar irin su Kofoworala,
(1977) wanda ya nuna wasan kwaikwayo a matsayin “Fasaha ce wadda ke samar da
jin da]i da annashuwa ga rayuwar ]an Adam”. A nan malamin ya nuna masu kallo na
samun jin da]i da annashawa wurin wasan kwaikwayo.
Crow, (1983) cewa ya yi “Wasan kwaikwayo wani
irin wasa ne a inda mutane kan kwaikwayi wasu mutane ko wasu abubuwa dangane da
halayen su ko irin abubuwan da suke gudanarwa. Ana iya yin wasa dan nisha]antarwa
ne ga masu kallo”.
Har ila yau, Dangambo, (1984) cewa ya yi
“Wasan kwaikwayo kamar yadda sunan ya nuna, wasa ne da aka gina kan kwaikwayon
wani labari ko wata matsala ta rayuwa da ake son isarwa ga jama’a a kan aiwatar
da labarin ko matsalar da sauransu, cikin siffar ya}ini wato a zahiri”.
Haka kuma, Ahmed (1985) ya ce “Wasan kwaikwayo
shi ne duk wata matsala da ta }unshi abu biyu. Na farko ta zamo wasa ne, ko
kuma abu ne wanda yake ba gaskiya ba ne lokacin da ake abin. Na biyu shi ne
wasan ya zama ma}asudinsa na sake kama ne. Ta wasan sake kamar nan, mai wasan
ko ‘yan wasa za su canja kamanninsu na yau da kullum.
Abdullahi (1986) a nasa bincike ya fa]i cewa;
“Wasan kwaikwayo shi ne abu wanda ba da gaske ba, amma mutane ke siffanta kansu
da shi ta hanyar wasa da kwaikwayo”.
Muhammad, (1989) ya bayyana cewa; “Wasan
kwaikwayo na nufin duk wani aiki, motsi, siffantawa da kamanta wani abu da wani
ya yi ko wata dabba ya yi ta cikin raha.
Haka kuma a bayanin Sambo (1990) ya nuna Adamu
Ibrahim Malunfashi ya ce “Wasan kwaikwayo koyi ne da yadda wani ko wasu ke yin
wani abu. A wajen koyin a iya samun canja kama, ko ta magana, ko tufafi da
sauransu. Wannan abin da ake yi ba da gaske ba ne”.
Yar Aduwa, (2008) ya bayyana ma’anar wasan kwaikwayo
da cewa “kamance ne na wasu halaye ko yanayin rayuwar ]an Adam wadda ake
gudanarwa a cikin raha da annashuwa don cimma wata manufa”.
Bugu-da-}ari, Yar ‘Aduwa (2008) ya sake cewa
“Wasan kwaikwayo hanya ce ta baje kolin halayen jama’a da yanayin rayuwarsu ta
cikin nisha]i da raha domin su gani su kuma za~i nagari su yi amfani da su
sannan su yi watsi da mummuna.
Shi kuma Gusau, (2009) ya ce “Wasan kwaikwayo
wata dabara ce wadda ake amfani da ita ta kwaikwayon wasu abubuwa wa]anda wasu
rukunoni na al’umma suke aiwatarwa ana yi masu hannunka-mai-sanda tare da yin
nuni cikin nisha]i.
[angambo (2011) yana cewa “Wasan kwaikwayo
wani labari ne ko wata matsala ta rayuwa da ake son nusarwa ga jama’a”.
Kamar yadda aka nazarta daga ma’anonin masana
daban-daban da kuma manazarta, an fahimci abu guda ga wasan kwaikwayo yana
tattare da abubuwa, kamar su koyi da sake-kama, da wasa da nisha]i da
annashuwa, sannan kuma abin da ba da gaske ba ne, kuma ana yi ne don wasu su gani
(‘yan kallo ko masu sauraro) sannan yana iya kasancewa garga]i ne ake yi musu.
Haka kuma ko da a aikace
aka gudanar da wasan kwaikwayo, za a fahimci cewa yana nan dai a matsayin wasa,
sannan kuma ana }o}ari ne a kamanta wata ]abi’ar rayuwa da ke aukuwa ta hanyar
amfani da harshe don isar da sa}o ga al’umma.
Samuwar Wasan Kwaikwayo Da Nau’o’insa
Masana sun bayyana babu wata magana ]aya
dangane da samuwar wasan kwaikwayo. Sun nuna wasan kwaikwayo abu ne mai
da]a]]en tarihi a duniya baki ]aya, kuma babu wani wanda zai bugi }irji ya ce
ga takamaiman ranar da aka fara wasan kwaikwayo. Akwai hasashe da wasu masanan
suka yi dangane da samuwar sa kamar haka:
Clark, (1966) ya bayyana cewa “Duk da cewa
babu wani ajiyayyen tarihi da ya nuna lokacin da aka fara wasan kwaikwayo, amma
ya ce akwai tabbacin wannan nau’i na adabi da]a]]en abu ne, kuma kusan kowace
}abila ta wannan }asa tana da shi. A nasa ra’ayin wai har za a iya raba wa]annan wasannin zuwa gida biyu.
Akwai wasannin da ake yi domin girmama abin bautarsu da wa]annan }abilu ke yi
wato kamar bautar da Kanawa suke yi wa Tsumbarbura
a }ar}ashin jagorancim Barbushe, ya ce wa]annan su ne na addinin. Akwai wanda
ake kira “masgaradas” wato na dodo da kuma irin wa]anda ake shiryawa
}ungiya-}ungiya a kowane shekara.
Ogunbiyi (1981) cewa ya yi “Ba wai babu wasan
kwaikwayo ba ne a Afirika ba, tun daga farko yadda za a tsare da aiwatar da shi
ne babu. A ta}aice samuwar wasan kwaikwayo a nahiyar Afirika ba zai rasa nasaba
da harkar bauta wanda mutane da suke aiwatarwa ba. Hakan yakan kasance saboda
ala}ar wannan bauta da wasu daga cikin tsarin wasa irin na kwaikwayo. Misali
canza kama da amfani da wasu tufafi na musamman da amfani da lokacin aiwatarwa
har ma da aiki da umurni”. A don haka a nahiyar Afirika abin da ya sa ake
danganta bauta da tushen wasan kwaikwayo shi ne irin sigogin wasan da bautar ta
ke ]auke da shi.
Waston (1983) cewa ya yi “Da wasan kwaikwayon
Girkawa da na Turawa sun samo asali ne daga bauta irin ta addini, kuma ma har
babu maganar addini a ciki, a ‘yan kwanakin nan ana iya sanya wasu abubuwa na
bauta da zarar ana bu}atar haka”. A wani }arin bayani kuma ci gaba da cewa ya
yi, “Wasan kwaikwayon Girkawa sannan da mai biye da shi watau na Turawa, dukkan
su sun samo asali wato tushensu na addini ne, kuma iyayen gijinsu (gumakansu)
suna da wata rawa ta musamman mai muhimmanci da suke takawa”. Wa]annan bayanai
guda biyu kusan dukkanninsu abu ]aya ne suke nunawa. Wato wasanin kwaikwayo na
Girkawa da wanda ake da shi a Turai duk daga abu guda suka faro wato addinin
su.
Holt da Winston (1983) sun tabbatar da cewa “Duk
inda ake wasan kwaikwayo musamman a tsohuwar daular Girkawa da Turai da Indiya
da kuma Japan, tushen sa ]aya ne. Ya taso ko ya samo asali ne daga bukukuwan
addini ta musayar zance ko wa}a tsakanin shugaba da ‘yan amshi ko kuma tsakanin
}ungiyar mawa}an addini. Sun bayyana Dynoysus a matsayin wani gunkin Girkawa ne
mai kula da tsiro, musamman itatuwa, kuma shi ne mai kula da giya ana ma
kiransa Bacchus. Wasannin raha da ban dariya sun samo asali ne daga bautar da
ake yi masa.
Ahmed, (1985) ya nuna cewa, Sengnor ya
tabbatar, “Wa}e da amshi da kuma raye-rayen wasan kwaikwayo na daular Girkawa
shekaru aru-aru a da, wa]anda asalin su wasannin kwaikwayon addinin Eleusian
ne, cewa ainihin tushensu shi ne bautar Osiris, wanda ake yi a Masar ta jerin
gwano, ana wa}e da amshi, ha]e da rawa”.
Yar Aduwa, (2007) ya kawo dalilai guda uku
wa]anda yake ganin su ne mafarin samuwar wasan kwaikwayo. Dalili na farko dai
shi ne wanda ya ke cewa an fara samun wasan kwaikwayo ne a dalilin bauta, watau
irin bukukuwa da ake yi wa abin da jama’a suke bautawa. A lokacin wannan bauta
ne shugabannin addini suke kwaikwayon ]abi’un wa]annan allolin nasu, to an ce
wai ta haka aka fara samun wasan kwaikwayo.
Dalili na biyu kuma shi ne wai akwai wa}o}i da
kirari da akan yi a lokacin binne jarumai, wanda yake bayanin irin halayensu na
jarunta, da kuma aka yi nisa wani lokaci har akan samu wani ko wasu mutane masu
zuwa suna kwaikwayon irin yadda wa]annan jarumai suke aiwatar da jarumtakarsu,
to an ce wai irin wannan kwaikwayo da suke yi a hankali shi ya haifar da yin
wasan kwaikwayo.
Dalili na uku kuma shi ne wai wasan kwaikwayo
ya samu ne a dalilin bayar da labari da ake wa mutane, misali a dandamali ko
kuma idan an je farauta, to a wannan lokaci akan ba wa mutane labarin jarumai
na wurin ya}i da kuma farauta, to an ce irin wannan labaru ne a hankali da ake
bayar da su da baki aka shiga kwaikwayon wa]annan jarumai, to sannu a hankali
wannan shi ma sai ya haifar da wasan kwaikwayo.
Ta yin la’akari da wa]annan dalilai da wannan masani
ya kawo ne ake ganin cewa su ne suka haifar da wasan kwaikwayo, kuma ana
kyautata zaton an fara wasan kwaikwayo ne a “Greek” wato }asar Girka kimanin
wajen shekaru ]ari shida (600) kafin haihuwar Annabi Isah (AS). Girkawa ne dai
suka fara yin wa}o}i da raye-raye don su girmama abin bautarsu wato “Dionysis” suna
yin wannan biki ne a lokacin na musamman don girmamawa tare da neman wata alfarma
a wajen ubangijin na su.
Yar’ aduwa, (2007) ya }ara da cewa a }asashen
Asiya kuwa an ce suna da wasannin kwaikwayonsu amma na kansu wanda ba su da
ala}a da }asashen Turai. Wa]annan wasannin suna gina su ne a bisa al’adunsu na
gargajiya zalla. Misali a }asar Indiya an ce suna daga cikin masu da]a]]an
tarihi na wasan kwaikwayo, kodayake ba a san ha}i}anin lokacin da aka fara
wa]annan wasanni ba, amma an fara samun wasannin tun daga shekaru 200 kafin
haihuwar Annabi Isa (Alaihis Salam). An ce wani mutum mai suna Bahara shi ne
mutumin da ya fara rubuta wasan kwaikwayo a Indiya, wasan mai suna
“Netyasastra”. Wannan shi ya bu]e }ofar samun wasannin kwaikwayo a Indiya
wa]anda yawancinsu masu ba da nisha]i da farin ciki suke shiryawa.
Haka kuma a }asar China (Sin) an ce wasannin
nasu sun samu asali ne daga wa}e-wa}e da raye-raye da ake yi domin girmama
abubuwan da suke bautawa. An fara samun wasan kwaikwayo a zamanin wani sarkinsu
mai suna Yua (1279-1368). Labarin haka
ya ke a }asar Japan a inda su ma wasannin kwaikwayonsu ya samo asali daga
lokacin bikin bauta da suke yi wa abun bautarsu. Wasan kwaikwayon da ya fi shahara
a lokacin shi ne mai suna “Kabuki” (Yar’aduwa, 2007).
A don haka a wasu al’umomin
Nijeriya wasan kwaikwayo asalinsa shi ma bai rasa nasaba da bukukuwan addini,
ko na tsare-tsare, da bukukuwan Yarbawa da na Inyamirai da wasannin dodonnin
ruwa na Owo da Ori na Ijaw. Saboda haka ta yin la’akari da wa]annan ra’ayoyi na
masana da manazarta da aka zayyana a baya za a fahimci kuma a yanke hukuncin
cewa lallai tarihin wasan kwaikwayo da]a]]e ne kuma mai tsawo. Babu shakka bauta
da addini sun taka muhimiyyar rawa wajen samuwa da kuma bun}asar wasan
kwaikwayo a fa]in duniya wanda ake cin moriyarsa har zuwa yau.
Nau’o’in Wasan Kwaikwayon Hausa
Wasan kwaikwayo a }asar Hausa yana da nau’o’in
sanannu guda biyu. Masana kamar su Yahaya (1987) da [angambo (2008) sun samu
daidaituwar ra’ayi a wannan ~angaren, sannan suka raba nau’o’in wasan kwaikwayo
kamar haka:
i.
Wasannin
kwaikwayo na Gargajiya
ii.
Wasannin kwaikwayo
na Zamani
Wasannin Kwaikwayo Na
Gargajiya
Wasannin kwaikwayo na gargajiya wasanni ne da
Bahaushiyar al’ada ta yarda da su, wa]anda daga cikin wasannin akan yi su, ko a gabatar da su a kowane lokaci. Wasu
kuma daga cikinsu akwai lokutan da ba a yin su, wasu kuma akan gabatar da su
shekara-shekara kuma akan yi su a wasu lokutan bukukuwan al’ada. A irin
wa]annan lokuta al’adar Bahaushe ta bada damar a yi wa]annan wasanni, wata}ila
domin murnar sake gewayowar wa]annan lokuta da kuma girmama su. Misali a
lokacin watan Azumi akan yi wasan tashe da kuma lokutan kaka inda akan yi wasan
bu]ar dawa da cin tumu da sauransu.
Akwai tanade-tanade da ake yi wa kowane wasa
ta yadda zai tafi daidai da kamannin wasa a al’adance. Misali, a wasannin
shekara-shekara na watan Azumi akwai wasanni daban-daban da akan yi duk lokacin
da watan Azumi ya kama goma da tsayawa, kamar wasannin tashe.
Za a iya cewa akwai al’adu da dama wa]anda
suka danganci wasan kwaikwayo. Ire-iren wa]annan al’adu kuwa sun ha]a da
wa]anda yara ko samari suke kwaikwayo tsakaninsu. Wa]annan su ne ake kira
wasannin kwaikwayo na gargajiya ko na asali.
A dangane da haka ne aka kawo ka]an daga cikin
ire-iren wasannin kwaikwayo na gargajiya da Hausawa ke yi tun kafin zuwan
addinin Musulunci. Da farko an kasa wasannin ne zuwa rukuni-rukuni kamar haka:
-
Wasannin
Kwaikwayo na Matasa: Shi wannan
rukunin ya }unshi ire-iren wasannin da matasa ke gudanarwa musamman ma a
dandali. Misalan ire-iren wasannin sun ha]a da; kalankuwa, Takkai, Jatau mai
magani wasan mairama da Dauda da sauransu.
-
Wasannin
Kwaikwayo na Masu Sana’a: Su ire-iren
wa]annan wasanni ne da ake danganta su da wata sana’a. Misalansu sun ha]a da;
Wasan ‘yan kama, wasan ‘yan hoto wasan
ma}era, wasan Mahauta.
-
Wasannin
Kwaikwayo na Lalura: Su wa]annan
wasannin akan shirya su ne a dalilin samuwar wata lalura watau idan wani abu ya
faru ake yin su, sai a da]e ba a yi wasan ba. Misalan ire-iren wasannin su ne
na ro}on ruwa, da kuma na husufi watau in rana ta kama wata.
-
Wasannin
Kwaikwayo na Tashe: Tashe al’ada ce
ta Hausawa da akan yi a cikin watan nan mai alfarma wato watan Ramadan. Tashe
wasa ne da ‘yan mata da samari watau yara }anana kan shirya shi a lokacin Azumi
ta yin kwaikwayon wasu abubuwa da kan faru a lokacin suna yin su bayan an sha ruwa
da nufin ba da nisha]i ga wa]anda suka yi Azumi. Ire-iren wa]annan wasannin
Tashe sun ha]a da; wasan mai ciki, mai }iriniya, kayi-rawa-kai-malam. Na ci na
kasa tashi, macukule da sauransu.
Wa]annan wasannin kwaikwayo su ne aka gada
kaka-da-kakanni kuma suna da matu}ar tasiri ga rayuwar Bahaushe domin kuwa
akwai darussa da dama da ake koyo a gare su. Haka kuma sukan cusa wa yara maza
da mata, samari da ‘yan mata tarbiyya tare da juriya da kuma jaruntaka.
Wasannin Kwaikwayo Na Zamani
Rubutaccen wasan kwaikwayo, da yake a rubuce
ake samar da shi, an san lokacin da aka fara yin sa. Abin mamaki a nan shi ne
wannan sashe na adabi bai samu ha~aka kamar sauran takwarorinsa ba, wato
rubutun zube da rubutattun wa}o}in Hausa. An yi wallafe-wallafe da dama a
rubutun zube da rubutattun wa}o}i wa]anda suka samu kar~awa sosai ga al’umma
fiye da rubutun wasan kwaikwayo.
Shi rubutaccen wasan kwaikwayo kuwa mai gajeren
tarihi ne, in an kwatanta shi da sauran ~angarori na adabin zamani na Hausa,
wannan ya sa ake ganin ya fi su }uruciya. Dalili kuwa shi ne addinin Musulunci bai
ba shi muhimmanci ba, kuma shi ya sa al’ummar Larabawa ba ta rubuta shi ba, sai
wajen }arni na 18 suka fara rubuta shi. A Hausa kuwa, an fara rubuta shi ne
bayan da Turawa suka zo har ma da wajen shekaru talatin da kama mulkinsu. Sai a
wajen shekara ta 1930 aka fara samar da littafin wasan kwaikwayon Hausa shida
“The six Hausa Plays” wanda wani Bature, mai suna R.M. East ya rubuta a 1930.
Haka kuma wasu su na ganin cewa an dai samu littafin wasan kwaikwayo da ]an
}asa Bahaushe ya rubuta a shekarar 1949, mai suna Wasan Marafa da Abubakar
Tunau ya rubuta kuma kamfanin NORLA, Zariya ya buga. Daga baya ne wasan
kwaikwayo ya ri}a ha~aka da gaske wanda har ya kasance ya kusa tarar da zube a
tsakanin 1971 zuwa 1974 da kuma tsakanin 1981 zuwa 1986 in an bi tsarin yadda
aka rubuta su.
A ta}aice rubutaccen wasan kwaikwayo na zamani
ya }unshi rassa guda shida, kamar haka: -
(a)
Wasan kwaikwayo
na littattafai
(b)
Wasan kwaikwayo
na Rediyo
(c)
Wasan kwaikwayon
Talbijin
(d)
Wasan kwaikwayo
na Silima/Majigi
(e)
Wasan kwaikwayo
na Dandamali
(f)
Wasan kwaikwayo
na Bidiyo / Fim
Wa]annan dukkaninsu nau’o’i
ne na rubutaccen wasan kwaikwayo wanda akan tsara su ne a rubuce kafin a
aiwatar da su a Talabijin ko Rediyo ko silima ko dandamali ko kuma a Fim. A don
haka wannan bincike zai karkata ne ga nazari a kan wasan kwaikwayo na Rediyo.